Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Zakariya 2

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Sa’an nan na ɗaga kai sai na ga mutum a tsaye riƙe da ma’auni a hannunsa!
2Sai na yi tambaya, na ce, “Ina za ka?” Ya amsa mini ya ce, “Zan je in auna Urushalima, in ga yadda fāɗinta da tsawonta suke.”
3Sai mala’ikan da yake yi mini magana ya tafi, sai wani mala’ika ya zo ya same shi
4ya ce masa, “Yi gudu, gaya wa saurayin can cewa, ‘Urushalima za tă zama birni marar katanga domin mutane da dabbobi masu yawa ƙwarai za su kasance a cikinta.
5Ni da kaina ne zan zama katangar wuta kewaye da birnin, in kuma zama darajarta,’ in ji Ubangiji.
6“Zo! Zo! Ku gudu daga ƙasar arewa,” in ji Ubangiji, “gama na warwatsa ku a kusurwoyi huɗu na sama,” in ji Ubangiji.
7“Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!”
8Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne.
9Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni.
10“Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji.
11“Ƙasashe da yawa za su haɗa kai da Ubangiji a ranan nan, za su kuma zama mutanena. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni gare ku.
12Ubangiji zai gāji Yahuda a matsayin rabonsa a cikin ƙasa mai tsarki zai kuma sāke zaɓi Urushalima.
13Ku yi tsit a gaban Ubangiji, dukanku ’yan adam, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.