Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Waƙar Waƙoƙi 7

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa.
2Cibinki kamar kwaf ne da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama wanda furen bi-rana ya kewaye.
3Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, tagwayen barewa.
4Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon kusa da ƙofar Bat Rabbim. Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon wadda take duban Damaskus.
5Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki.
6Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!
7Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace.
8Na ce, “Zan hau itacen dabino; zan kama ’ya’yansa.” Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,
9kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.
10Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne.
11Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, bari mu kwana a ƙauye.
12Bari mu tafi gonar inabi da sassafe don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya, ko furanninsu sun buɗe, ko rumman sun yi fure, a can zan nuna maka ƙaunata.
13Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.