Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Waƙar Waƙoƙi 3

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Dare farai a kan gadona na nemi wanda zuciyata take ƙauna; na neme shi amma ban same shi ba.
2Zan tashi yanzu in zagaya gari, in ratsa titunansa da dandalinsa; zan nemi wanda zuciyata take ƙauna. Saboda haka na neme shi, amma ban same shi ba.
3Masu tsaro suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni, sai na ce, “Kun ga mini wanda zuciyata take ƙauna?”
4Rabuwata da su ke nan sai na sami wanda zuciyata take ƙauna. Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, zuwa ɗakin wadda ta yi cikina.
5’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
6Wane ne wannan mai zuwa daga hamada kamar tunnuƙewar hayaƙi, cike da ƙanshin turaren mur da lubban da aka yi da kayan yajin ’yan kasuwa?
7Duba! Abin ɗaukar Solomon ne, jarumawa sittin suke rakiya, zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila,
8dukansu suna saye da takobi dukansu ƙwararru ne a yaƙi, kowanne da takobinsa a rataye a gefensa, a shirye don abubuwan bantsoro na dare.
9Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka; ya yi shi da katako daga Lebanon.
10An yi sandunansa da azurfa, aka yi ƙasarsa da zinariya. An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya, ’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna.
11Fito, ku ’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.