Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Zabura 97

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.
2Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.
3Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.
4Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.
5Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.
6Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.
7Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli!
8Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.
9Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli.
10Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
11An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.
12Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.