Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Zabura 92

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,
3da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.
4Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
5Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
6Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,
7cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.
8Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.
9Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
10Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.
11Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.
12Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
13da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
14Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,
15suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.