Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Zabura 132

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
2Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
3“Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba,
4ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna,
5sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
6Mun ji haka a Efrata, muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,,
7“Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
8ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
9Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”
10Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka.
11Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,
12in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”
13Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,
14“Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
15zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci.
16Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.
17“A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
18Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.