Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Zabura 116

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.
2Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.
3Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai.
4Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”
5Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.
6Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.
7Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.
8Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe,
9don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.
10Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.”
11Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”
12Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?
13Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji.
14Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa.
15Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.
16Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.
17Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
18Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,
19a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.