Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Zabura 108

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Zuciyata tsayayyiya ce, ya Allah; zan rera in kuma yi kiɗi da dukan raina.
2Ku farka, garaya da molo! Zan farkar da rana.
3Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai cikin mutane.
4Gama ƙaunarka da girma take, bisa fiye da sammai; amincinka ya kai sarari.
5A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.
6Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
7Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Ciki nasara zan raba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.
8Gileyad nawa ne, Manasse nawa ne; Efraim shi hulan kwanona, Yahuda ne sandana na sarauta.
9Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”
10Wa zai kawo ni birni mai katanga? Wa zai jagorance ni zuwa Edom?
11Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
12Ka ba mu taimako a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.
13Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattaka abokan gābanmu.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.