Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Mika 3

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Sa’an nan na ce, “Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila. Ya kamata ku san shari’a,
2ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta, ku da kuke feɗe mutanena kuke tuge nama daga ƙasusuwansu;
3ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”
4Sa’an nan za su kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa musu ba. A wannan lokaci zai ɓoye fuskarsa daga gare su saboda irin muguntar da suka yi.
5Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari.
6Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba, kuma duhu, ba tare da duba ba. Rana za tă fāɗi wa annabawa, yini kuma zai zama musu duhu.
7Masu gani za su ji kunya, masu duba kuma za su ji taƙaici. Dukansu za su rufe fuskokinsu gama ba amsa daga Allah.”
8Amma game da ni, ina cike da iko ta wurin Ruhun Ubangiji da kuma adalci da ƙarfi, don a sanar da Yaƙub laifofinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa.
9Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila, ku da kuke ƙyamar gaskiya, kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;
10kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta.
11Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.”
12Don haka, saboda ku, za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma ta zama tarin juji, tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.