Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Yoshuwa 20

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,
2“Ka gaya wa Isra’ilawa su keɓe waɗansu birane su zama biranen mafaka kamar yadda na umarce ku ta wurin Musa,
3domin idan wani ya kashe wani bisa kuskure ba da niyyar yin kisankai ba, mutumin zai iya gudu zuwa can yă fake don kada a kashe shi.
4Lokacin da ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen nan, sai yă tsaya a ƙofar birnin yă gaya wa dattawan wannan birni damuwarsa. Sa’an nan su karɓe shi su ba shi wurin zama a cikin birninsu.
5In mai neman yă kashe shi don ramako ya bi shi zuwa can, ba za su miƙa shi ba domin ba da niyya ya kashe wani ba, kuma ba fushi ne ya sa ya yi kisan ba.
6Zai zauna a wannan birni har sai taron jama’a sun yi masa shari’a, kuma har sai lokacin da babban firist wanda yake aiki a lokacin ya mutu, sa’an nan zai iya koma garinsa na dā.”
7Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda.
8A hayin Urdun, gabas da Yeriko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ruben, Ramot cikin Gileyad a kabilar Gad, da Golan cikin Bashan a kabilar Manasse.
9In wani mutumin Isra’ila ko kuma wani baƙon da yake zama a cikinsu, ya yi kisankai cikin kuskure, zai iya gudu zuwa biranen da aka keɓe, ba za a bari mai neman ramako yă kashe shi kafin jama’a su yi masa shari’a ba.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.