Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Ayuba 17

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana.
2Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.
3“Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari. Wane ne zai kāre ni?
4Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.
5In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada ’ya’yansa za su makance.
6“Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.
7Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki; jikina ya zama kamar inuwa kawai
8Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro; marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.
9Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.
10“Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa! Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.
11Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so.
12Mutanen nan sun juya rana ta zama dare. A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’
13In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,
14In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
15To, ina begena yake? Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
16Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.