Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Ishaya 46

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa; ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne. Siffofin da ake yawo da su nawaya ne, kayan nauyi masu gajiyarwa.
2Sun durƙusa suka kuma rusuna tare; ba su iya kuɓutar da nauyin kaya su kansu sukan tafi bauta.
3“Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku.
4Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.
5“Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni? Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?
6Waɗansu sukan zubar da zinariya daga jaka su kuma auna azurfa a ma’auni; sukan yi haya maƙerin zinariya don yă ƙera allah, su kuma rusuna su yi masa sujada.
7Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi; sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya. Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba. Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa; ba zai iya cetonsa daga wahala ba.
8“Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya, ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye.
9Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā; ni ne Allah, kuma babu wani; ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.
10Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.
11Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta; daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina. Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru; abin da na shirya, shi zan aikata.
12Ku kasa kunne, ku masu taurinkai, ku da kuke nesa da adalci.
13Ina kawo adalcina kusa, ba shi da nisa; kuma cetona ba zai jinkirta ba. Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.