Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Ishaya 31

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.
2Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.
3Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare.
4Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.
5Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”
6Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.
7Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.
8“Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba; takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye. Za su gudu daga takobi za a kuma sa samarinsu aikin dole.
9Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.