Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (HAUBIB, 2020)

Fitowa 24

Karanta Littafi Mai Tsarki a Hausa. Nazarin Divine Threads a Hausa yana nan tafe.

1Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ku hauro zuwa wurina, kai da Haruna, Nadab da Abihu, da kuma dattawa saba’in a cikin Isra’ila. Za ku yi sujada da ɗan nisa,
2sai Musa kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama’a su hau tare da shi.”
3Sa’ad da Musa ya tafi ya faɗa wa mutanen duk kalmomin Ubangiji da dokokinsa, sai suka amsa da murya ɗaya suna cewa, “Duk abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi.”
4Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.
5Sai ya aiki samarin Isra’ilawa, suka miƙa hadaya ta ƙonawa, suka kuma miƙa ƙananan bijimai don hadaya ta salama ga Ubangiji.
6Musa ya ɗauki rabin jinin ya zuba a cikin kwanoni, rabin kuma ya yayyafa a kan bagaden.
7Sa’an nan ya ɗauki Littafin Alkawari ya karanta wa mutane. Suka amsa suka ce, “Za mu yi duk abin da Ubangiji ya faɗa; za mu yi biyayya.”
8Musa ya kuma ɗauki jinin, ya yayyafa a kan mutanen ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, bisa ga dukan waɗannan kalmomi.”
9Musa da Haruna, Nadab da Abihu, da dattawa saba’in, Allah na Isra’ila suka haura
10suka kuma ga Allah na Isra’ila. A ƙarƙashin ƙafafunsa akwai wani abu wanda aka yi da saffaya, mai haske kuma kamar sararin sama kansa.
11Amma Allah bai yi wa shugabannin Isra’ila wani abu ba; suka ga Allah, suka ci suka kuma sha.
12Ubangiji ya ce wa Musa, “Hauro wurina a kan dutse, ka tsaya a nan, zan ba ka allunan dutsen, da doka da umarnan da na rubuta don koyonsu.”
13Sa’an nan Musa ya fita tare da Yoshuwa mataimakinsa, ya kuwa hau kan dutsen Allah.
14Ya ce wa dattawan, “Ku jira mu a nan, sai mun dawo wurinku. Haruna da Hur suna tare da ku, in wani yana da wata damuwa, sai yă je wurinsu.”
15Da Musa ya hau dutsen, sai girgije ya rufe dutsen,
16sai ɗaukakar Ubangiji ta sauka a kan Dutsen Sinai, kwana shida girgije ya rufe dutsen, a rana ta bakwai, sai Ubangiji ya kira Musa daga cikin girgijen.
17Ga Isra’ilawa dai, ɗaukakar Ubangiji ta yi kamar wuta mai ci a kan dutse.
18Sa’an nan Musa ya shiga girgijen ya hau kan dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba’in da dare arba’in.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ — Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ — Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Tushe: eBible.org/hausa. Lasisi: CC BY-SA 4.0. Ana nuna ayoyin a cikin jerin surori ba tare da kanun labarai da bayanin ƙasa ba; ba a sake rubuta kalmomin ayoyin ba. Ana bayar da nunin rubutun Littafi Mai Tsarki ƙarƙashin CC BY-SA 4.0, dabam da rubutun nazarin Divine Threads. The original work by Biblica, Inc. is available free at www.biblica.com and open.bible.